29 Janairu 2026 - 22:07
Source: ABNA24
Amurka Tana Ci Gaba Da Tattara Makaman Yakinta A Gabas Ta Tsakiya.

Jiragen sama uku na rundunar sojin saman Amurka C-17A Globemaster suna kan hanyarsu ta zuwa Gabas ta Tsakiya, suna isowa daga Rota, Spain, da Prestwick, Birtaniya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wani jirgin saman soja na Amurka, C-5 Super Galaxy, shi ma yana gab da yankin, tare da na'urar bin diddigin sa.

Ta fuskacin Iran kuwa Mai magana da yawun rundunar kare juyin juya halin Iran Brigadier Janar Ali Mohammad Naeini: "Mun shirya wa dukkan yanayi. Yaƙin kwanaki 12 ya tabbatar da cewa zaɓin soja a kan Iran ya gaza, kuma sojojinmu za su tantance sakamakon yaƙin".

A gefen Isra’ila kuwa: Hukumar Watsa Labarai ta Isra'ila (Kan) ta ruwaito, tana ambaton majiyoyi, cewa Isra'ila a shirye take ta bayar da duk wani taimako ga Amurka game da Iran.

A zahiri, Washington ba ta buƙatar taimakon Isra'ila, ba kamar Isra'ila ba.

Manufar bayar da taimako ita ce tunzura Trump ya kai hari, wanda Isra'ila ke so amma ba za ta iya aiwatar da shi ita kaɗai ba. Yaƙin kwanaki 12 sheda ne kana haka.

Isra'ila ta yi imanin cewa adawar yanki da na ƙasa da ƙasa ga yaƙin Amurka da Iran cikas ne ga burinta.

Your Comment

You are replying to: .
captcha